Jakadan Najeriya ya yabawa Shugaba Buhari kan sabuwar Doka mai baiwa Matasa dama a harkokin Siyasa

Jakadan Najeriya ya yabawa Shugaba Buhari kan sabuwar Doka mai baiwa Matasa dama a harkokin Siyasa

Mun samu cewa jakadan Najeriya a 'kasar Amurka, Alkali Sylvanus Nsofor, ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari dangane da sabuwar dokar nan da take baiwa matasa dama ta damawa cikin harkokin siyasa da shugabanci a kasar nan.

Nsofor yayi wannan yabo ne yayin halartar taron Matasan Shugabanni na duniya kasancewar sa babban bako na musamman da aka gudanar a shelkwatar Majalisar 'Dinkin Duniya dake birnin New York na kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, a watan Mayun shekarar da ta gabata ne shugaba Buhari ya rattaba hannu kan sabuwar dokar da take baiwa matasa dama ta damawa cikin harkokin siyasa bayan ta samu sahalewar majalisar dokoki ta tarayya.

Dangane da kidayar al'ummar Najeriya da aka gudanar a shekarar 2006 da ta gabata, bincike ya tabbatar da cewa kaso 70 cikin 100 na al'ummar Najeriya sun kunshi Matasa wanda shine babban arziki ga kowace kasa ta fuskar samuwar ci gaba.

Jakadan Najeriya ya yabawa Shugaba Buhari kan sabuwar Doka mai baiwa Matasa dama a harkokin Siyasa

Jakadan Najeriya ya yabawa Shugaba Buhari kan sabuwar Doka mai baiwa Matasa dama a harkokin Siyasa
Source: Depositphotos

Jakadan yake cewa, Matasan kowace kasa su ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da hadin kanta da ci gaba ta fuskar tattalin arziki, zamantakewa da kuma haɗin kai na tabbatuwar siyasa.

Mista Nsofor ya lura cewa, ba bu wata kasa da ta kai munzali na samu ci gaba face sai da ta tabbatar ta gina makomar ta bisa kyawawan tsare-tsare da ta kafa da kuma shimfidar managarciyar turba domin matasan ta.

KARANTA KUMA: Sojoji sun Kashe 'yan Baranda 5 tare da cafke muggan Makamai a Birnin Gwari

Legit.ng ta fahimci cewa, sabuwar dokar da shugaba Buhari da majalisar dokoki ta tarayya suka amince a kai ta na baiwa matasa da suka kai shekaru 35 dama ta neman kujerar shugaban kasa sabanin yadda take a baya na shekaru 40.

Kazalika sabuwar dokar ta yarjewa matasa masu shekaru 30 wajen neman kujerar gwamna ko kuma sanata sabanin yadda dokar take a baya na shekaru 30, inda kuma ta bayar da dama ga matasa masu shekaru 25 su nemi kujerun majalisun dokoki na jihohin su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel