Sanatocin PDP sun koma kiyamul laili a majalisa kan Saraki

Sanatocin PDP sun koma kiyamul laili a majalisa kan Saraki

Sanatocin jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP sun koma kwana a cikin majalisar dokokin tarayya domin tsoron kada sanatocin hamayya na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun tsige Saraki, wani sanata ya bayyana.

Sanata Philip Gyunka mai wakiltar mazabar Nasarawa ta Arewa wanda yayi jawbi a garin Lafiya jiya ya bayyana hakan ne yayin mia wasikar nuna aniyar takaran kujeran gwamnan jihar Nasarawa karashin jam’iyyar PDP.

Yace: “ Na tashi da safen nan bayan kiyamul-laili kuma zan koma da dare domin cigaba da kiyamul lailin.

Muna zagayen kwana a majalisa tsakninmu. Game da tsiga da suka cewa, ba zai yiwu ba saboda kasashen waje na sane da abubuwan da sukeyi.”

KU KARANTA: ‘Yan garkuwa da mutane sun sace mata da dan malamin kwaleji a Zamfara

Kada gabanku ya fadi. Za su baku tsoro kamar yadda suke bamu. Kamar ni yanzu, ba zan iya kirga iyakan da suka kirani ba. Bami san sun zo ruguzu demokradiyya bane. Amma shugaban majalisar dattawa matsayin kyakyasan PDP zai kawo mana ceto.”

“Sun dade suna kokarin yin hakan amma sun gaza. Na san ba zasu daina ba amma ba zasu samu nasara ba saboda na san Najeriya ba zasu barsu su zub da mutuncin demokradiyya ba.”

Har ila ana takun sako tsakanin mambobin jam’iyyar PDP da APC a majalisar dokokin tarayya kan tsige shugaban majalisar, Bukola Saraki. Yayinda yan jam’iyyar APC ke jiran a dawo zauren majalisa su tsigeshi, Bukola Saraki ya ki bari majalisa ta dawo tsoron hakan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel