Yanzu Yanzu: An nada Nnochirionye Afunanya a matsayin sabon kakakin hukumar DSS

Yanzu Yanzu: An nada Nnochirionye Afunanya a matsayin sabon kakakin hukumar DSS

Hukumar yan sandan farin kaya (DSS) ta sanar da nadin Nnochirionye Afunanya a matsayin sabon kakakinta.

Nadin na kunshe ne a wata sanarwa daga sashin hulda da jama’a na hukumar dake Abuja, a ranar Alhamis, 16 ga watan Agusta, jaridar Punch ta ruwaito.

Yanzu Yanzu: An nada Nnochirionye Afunanya a matsayin sabon kakakin hukumar DSS

Yanzu Yanzu: An nada Nnochirionye Afunanya a matsayin sabon kakakin hukumar DSS

Mukaddashin darakta janar na hukumar, Mathew Seiyefa da yake zantawa da manema labarai a hedkwatar hukumar na kasa dake Abuja yayi alkawarin cewa zai nada kakakin hukumar.

KU KARANTA KUMA: Daga Buhari har Lalong zasu kai labari a 2019 – Kakakin majalisar dokokin jihar Plateau

Tsawon shekaru uku da dakataccen darakta janar na hukumar, Lawal Daura yayi yana shugabanci a wajen babu wani da aka sani a matsayin kakakin hukumar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel