Dan takarar kujerar shugaban kasa a APC ya bukaci mambobin jam’iyyar da su dakatar da kudirin tazarcen Buhari

Dan takarar kujerar shugaban kasa a APC ya bukaci mambobin jam’iyyar da su dakatar da kudirin tazarcen Buhari

Wani dan takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Dr. Sylvester Ogbonna yayi watsi da rahoton da fadar shugaban kasa tayi na cewa kasashen duniya na farin ciki da shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ogbonna a wata sanarwa da ya saki a jiya yace zancen gaskiya a siyasar duniya shine cewa Buhari baida cikakken baya a kudirinsa na sake takara karo na biyu.

Yace rashin cikakken lafiyar shugaban kasa, rashin cikakken makama, kashe-kashe, rashin bin doka na daga cikin abunda yasa shugaban kasar baida cikakken goyon baya.

Dan takarar kujerar shugaban kasa a APC ya bukaci mambobin jam’iyyar da su dakatar da kudirin tazarcen Buhari

Dan takarar kujerar shugaban kasa a APC ya bukaci mambobin jam’iyyar da su dakatar da kudirin tazarcen Buhari

Ya kara da cewa har ila yau matsalar rabuwar kai da na rashin daidaito a kasar na daga cikin gazawarsa.

KU KARANTA KUMA: Sauya sheka a karkashin Buhari ya banbanta da na Jonathan – Mataimatin shugaban APC

Ya kalubalanci shugaban kasar da ya kula da kasar da jam’iyyar kafin shi kansa. Inda ya bayyana cewa abu mafi muni da ka iya samun kasar a yanzu shine bari jam’iyyar PDP ta koma kan mulki.

Saboda haka yayi kira ga shugaban kasar da ya hakura mulki a haka cewa makomar APC yanzu na matasa ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel