Osinbajo ya jagoranci Zaman Majalisar Tattalin Arziki

Osinbajo ya jagoranci Zaman Majalisar Tattalin Arziki

Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a ranar Alhamis ta yau ya jagoranci zaman majalisar tattalin arziki na kasa da ya hadar da gwamnoni, ma'aikatun gwamnatin tarayya masu ruwa da tsaki da kuma babban bankin Najeriya.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ta bayyana, tattaunawar da ta gudana yayin wannan zama ta hadar da ababen da suka shafin tsaro kasar nan.

Wadanda suka halarci zaman majalisar sun hadar da, Shugaban tsaro Janar Gabriel Olanisakin, Shugaban hafsin sojin kasa Laftanar Janar Tukur Buratai, Shugaban hafsin sojin ruwa Ibok Ekwe Ibas, shugaban hasfsin sojin sama Abubakar Sadique, shugaban hukumar NIA Ahmed Abubakar da kuma Sufeto Janar na 'Yan sanda Ibrahim Idris.

Kusoshin gwamnati da suka halarci zaman sun hadar da; Sakataren gwamnati Boss Mustapha, Babban mai bayar da shawara kan harkokin tsaro Babagan Mongunu, Ministar Kudi Kemi Adeosun, Ministan Kasafi da tsare-tsaren kasa Udoma Udo Udoma da kuma babban akawun kasa, Ahmed Idris.

Osinbajo ya jagoranci Zaman Majalisar Tattalin Arziki

Osinbajo ya jagoranci Zaman Majalisar Tattalin Arziki

Gwamnonin da suka halarci ganawar yayin hada wannan rahoto da misalin karfe 11.20 na safiyar yau a fadar ta shugaban kasa sun hadar da; Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Abubakar Yari, Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom, Willy Obiano na jihar Anambra, Dave Umahi na jihar Ebonyi, Aminu Bello Masari na jihar Katsina, Rotimi Akeredelo na jihar Ondo da kuma Abubakar Bello na jihar Neja.

KARANTA KUMA: Kishin Ci gaban Najeriya ya sanya nake muradin Kasancewa Shugaban 'Kasa - Atiku

Sauran gwamnonin sun hadar da; Mallam Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna, Abubakar Badaru na jihar JIgawa, Simon Lalong na jihar Filato, Akinwumi Ambode na jihar Legas da kuma Mataimakan gwamnonin jihar Bayelsa, Rivers, Ogun, Oyo Benuwe da kuma wakilin gwamnan jihar Kano.

Legit.ng ta fahimci cewa, Babatunde Fowler, shugaban babban ma'aikatar samar da kudaden shiga ta kasa watau Federal Inland Revenue ya halartci zaman majalisar inda gwamnan jihar Jigawa ya bude taron da addu'a.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel