Wata sabuwa: Goodluck Jonathan ya kwato yan matan Chibok daga hannun Boko Haram

Wata sabuwa: Goodluck Jonathan ya kwato yan matan Chibok daga hannun Boko Haram

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya ceto yan matan Chibok da dama daga hannun mayakan Boko Haram, sai dai bai yarda ya fallasa hakan ba, don kare rayukan yan matan.

Legit.ng ta ruwaito tsohon Kaakakin tsohon shugaban kasa Jonathan, Ruben Abati ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 16 ga watan Agusta a yayin wata hira da yayi da Kaakakin shugaba Buhari, Femi Adesina a gidan talabijin na Arise.

KU KARANTA: Muna shan ɗan-karan tambaya daga hannun jami’an hukumar EFCC – Inji Gwamna Samuel Ortom

Wata sabuwa: Goodluck Jonathan ya kwato yan matan Chibok daga hannun Boko Haram

Abati da Adesina

“Mun ceto yan matan Chibok da dama, sai dai mai baiwa shugaban kasa shawara akan lamurran tsaro, Sambo Dasuki ya shawarci Jonathan akan kada a fallasa ceto yan matan, saboda a kare rayukansu, da na aka yi wannan, ba sau daya ba, bas au biyu ba.” Inji Abati.

Abati ya cigaba da fada ma Adesina “ba sau daya ba, bas au biyu ba, an kawo ma Jonathan yan matan, har ma ya baiwa wasu daga cikinsu tallafin karatu a jami’o’in kasashen Amurka da na Birtaniya, an umarce mu da kada mu sake mau fallasa labarin don kare yan matan, amma sai gashi naga kuna ta rawa wai don kun ceto wasu yan kalilan.”

Daga karshe Abati ya kalubalanci Adesina da idan ya musa ya tafi hukumar tsaro ta sirri, DSS, don ya tabbatar da hakan, a cewarsa suna da duk bayanan da suka shafi ceto yan matan a zamanin Jonathan.

A ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014 ne mayakan Boko Haram suka yi awon gaba da yan matan sakandarin makarantar kwana ta garin Chibok dake jihar Borno su 276, zuwa yanzu gwamnatin Buhari ta ceto guda 163 daga cikinsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel