Sojoji sun Kashe 'yan Baranda 5 tare da cafke muggan Makamai a Birnin Gwari

Sojoji sun Kashe 'yan Baranda 5 tare da cafke muggan Makamai a Birnin Gwari

- Hukumar sojin kasa ta kashe gawurtaccen 'Dan Ta'adda, Sani Dambuzuwa na jihar Zamfara

- 'Yan ta'adda sun salwantar da rayuwar wani dakarun soji 1 tare da raunata 2

- Hukumar Sojin ta samu nasarar cafke 'yan ta'adda da dama tare da muggan makamai

Wasu rahotanni da sanadin shafin jaridar Vanguard sun bayyana cewa, dakarun sojin kasa na Najeriya sun samun nasarar salwantar da rayuwar wasu 'yan baranda biyar da ake zargin 'yan fashi da makami ne da suka addabi matafiya a kan babbar hanyar nan ta garin Birnin Gwari.

Hukumar sojin ta samu wannan nasara ne yayin wata musayar wuta da 'yan ta'addan bayan sun yi ma su kwanton bauna da shigo-shigo ba bu zurfi inda ta kuma sheke wani gawurtaccen dan ta'adda da ya shahara a jihar Zamfara mai sunan Sani Danbuzuwa.

Rundunar sojin kasa ta kuma rasa jami'in ta guda da jikkatar wadansu guda biyu a yayin aukuwar wannan artabu a ranar Talatar da ta gabata kamar yadda wata sanarwa da sa hannu mataimakin kakakin rundunar sojin Muhammad Dole ta bayyana.

Sojoji sun Kashe 'yan Baranda 5 tare da cafke muggan Makamai a Birnin Gwari

Sojoji sun Kashe 'yan Baranda 5 tare da cafke muggan Makamai a Birnin Gwari

Legit.ng ta fahimci, hukumar sojin ta gudanar da wannan dauki ba dadi ne yayin amsa wani kira na gaggawa domin kai dauki ga al'umma yayin da 'yan fashi da makami gami da masu garkuwa da mutane suke cin karen su babu babbaka a babbar hanyar Funtuwa zuwa Birnin Gwari.

KARANTA KUMA: Buhari ba ya da cikakkiyar Lafiya ta Jagorancin 'Kasar Najeriya - Tambuwal

Dakarun sojin sun kuma fatattaki wannan 'yan ta'adda inda suke arce zuwa wani daji na Kwuyambana dake jihar Zamfara, yayin da dakarun da suka raunata ke karbar magani asibitin soji dake garin Kaduna kamar yadda Kanal Dole ya bayyana.

Kazalika rundunar sojin ta samu nasarar cafke muggan makamai na kare dangi da 'yan ta'adda suke tsere suka bari yayin neman mafaka ta tsertar da rayukan su. Hukumar ta kuma samu nasarar cafke wani kasurgumin mai garkuwa da mutane, Yunusa Suleiman a kauyen Sabuwa tun a ranar 14 ga watan Agustan da ya gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel