Majalisar dokokin jihar Niger ta sanya kujerar dan majalisa a kasuwa kan sauya sheka da yayi daga APC

Majalisar dokokin jihar Niger ta sanya kujerar dan majalisa a kasuwa kan sauya sheka da yayi daga APC

Majalisar dokokin jihar Niger ta kaddamar da kujerar Danladi Iyah a kasuwa sakamakon murabus da yayi daga jam’iyyar All Progressives Congress da kuma yayata cewa guguwar sauya sheka daga jam’iyyar zai kawo ziyara majalisar a kwanan nan.

Jaridar This Day ta rahoto cewa Iyah bai bayyana jam’iyyar adawa da yake shirin komawa ba.

Legit.ng ta tattaro cewa ya gabatar da takardan ajiye aikinsa ga shugaban jam’iyyar na jihar, Jibrin Imam, inda a ciki ya bayyana dalilinsa na barin APC a matsayin “tozarcin da nake fuskanta yayinda nake a jam’iyyar APC.”

An tattaro cewa yayin martani ga wasikar Iyah, APC ta aika wasika ga majalisar dokokin inda ta bukaci a sanya kujerar dan majalisar a kasuwa.

Majalisar dokokin jihar Niger ta sanya kujerar dan majalisa a kasuwa kan sauya sheka da yayi daga APC

Majalisar dokokin jihar Niger ta sanya kujerar dan majalisa a kasuwa kan sauya sheka da yayi daga APC

A cewar shugaban jam’iyyar dalilin da dan majalisar ya bayar bai isa dalili ba yafi kama da son zuciya ba wai kundin tsarin mulki ba.

KU KARANTA KUMA: NYSC ta saki sunayen yan bautar kasa 9 da suka nutse a ruwa a Taraba

A lokacin da shugaban APC ya karanto wasikar a gaban majalisar a ranar Laraba, 15 ga watan Agusta, wani mamba mai wakiltan mazabar Borgu, Alhaji Bala Ahmed Abba ya goyi bayan wasikar cewa ajiye aikin abokin aikin nasa baya bisa ka’ida.

Kakakin majalisar, Ahmed Marafa Guni ya umurci magatakardan majalisar da ya sanar da shawarar ga hukumomin da suka dace.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel