Za mu yi wa Kwankwaso da Shekarau adalci a Kano – PDP

Za mu yi wa Kwankwaso da Shekarau adalci a Kano – PDP

A daidai lokacin da guguwar iskar zaben 2019 ke gabatowa, kowace jam’iyya na kokarin ganin ta hada kan yayanta domin su yi gudu tare sannan su tsira tare.

Kamar yadda aka sani hadin kai na da matukar muhimmanci wajen nasarar zaben jam’iyya, inda a yanzu haka jam’iyyar PDP wacce it ace babbar jam’iyyar adawa a kasar ke kokarin ganin ta kwace mulki daga hannun APC a 2019.

Jam’iyyar PDP a jihar Kano na kunshe da wasu manyan bangarorin siyasa uku, inda kowane gida ke tinkaho da mabiyansa.

Wadannan 'yan siyasa sun hada da tsohon gwamna Rabi`u Musa Kwankwaso da Malam Ibrahim Shekarau da kuma tsohon minista, Aminu Wali.

Za mu yi wa Kwankwaso da Shekarau adalci a Kano – PDP

Za mu yi wa Kwankwaso da Shekarau adalci a Kano – PDP

Duk da cewa sun hade a jam`iyya daya a yanzu, hasashe sun nuna cewa sun sha bambam da junansu ta fannin akida.

Sanata Mas`ud El-Jibrin Doguwa shi ne shugaban jam`iyyar PDP na jihar Kano.

Ya ce dawowar tsoffin yan jam'iyyar a yanzu za ta taimaka masu wajen aiwatar da abin da ba a taba yin irin sa a siyasar Kano ba.

Babu dai wanda ya yi tsammanin cewa tsoffin gwamnonin biyu za su kulla kawance karkashin inuwar jam'iyya guda.

KU KARANTA KUMA: Sauya sheka a karkashin Buhari ya banbanta da na Jonathan – Mataimatin shugaban APC

Sai dai a wannan lokaci da ake ganin cewa jam'iyyar PDP na kunshe da wasu manyan gidajen siyasa.

Sanata Mas'ud ya ce a matsayin sa na shugaba wanda kuma ake sa ran ya yi adalci, duk wanda ya tsaya takara a wadanan bangarori uku kuma jama'a suka nuna shi suke so, to shi za su bai wa takara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel