Ana aikin Allah ya buge da aikin ‘yan ta’adda: An cafke wani da yunkurin tada bam a Saudiyya

Ana aikin Allah ya buge da aikin ‘yan ta’adda: An cafke wani da yunkurin tada bam a Saudiyya

- Adaidai lokacin da Musulmai suka himmatu don gudanar da aaikin Hajjin bana, wani, wani ashe yana can yana na shi shirin

- Bayan gano mugun nufin na mutumin, nan take ‘yan sanda suka dirka masa harsashi

A yau Alhamis ne jami'an tsaron kasar Saudiyyasuka damke wani dan kasar da yake yunkurin kaddamar da harin ta’addanci.

Kamfanin dillancin labarai na kasar ne ya rawaito yadda al’amarin ya kaya tsakanin jami’an tsaro da kuma mutumin.

Ana aikin Allah ya buge da aikin ‘yan ta’adda: An cafke wani da yunkurin tada bam a Saudiyya

Ana aikin Allah ya buge da aikin ‘yan ta’adda: An cafke wani da yunkurin tada bam a Saudiyya

Wanda ake zargin dai an an hango shi tamkar ya nade jikinsa da rigar bam sannan ya rika harbi inda jami’an ‘yan sanda suke, a cewar ministan harkokin cikin gida.

KU KARANTA: Wasu tsageru sun wawushe kudin sadakar da aka tara a wurin bauta

Ministan ya kara da cewa don haka ne jami’an tsaron suka harbi shi wanda ake zargin domin su kama shi. Sai dai ba'a bayyana suna ko kabilar wanda ake zargin ba.

Wannan lamari dai ya faru da kusan Asubahin yau a arewacin garin Al Bukayriyah, kuma babu wani jami’in tsaro ku mutanen gari da artabun ya raunata, sannan an kwato duk makaman dake wurinsa masu yawa.

Kasar Saudiyya dai na fama da hare-haren ‘yan tada kayar baya wanda ya fara kamari a baya-bayan nan, inda ake yunkurin kaiwa wurare masu tsarki hari.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel