Kishin Ci gaban Najeriya ya sanya nake muradin Kasancewa Shugaban 'Kasa - Atiku

Kishin Ci gaban Najeriya ya sanya nake muradin Kasancewa Shugaban 'Kasa - Atiku

A ranar Larabar da ta gabata ne tsohon Mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa tsanani na kishin 'kasar Najeriya ya sanya yake muradi da zumuɗin na ci gaba da jajircewa wajen neman kujerar shugaban kasa.

Tsohon Mataimakin shugaban kasar yake cewa, ko shakka babu babban dalilin da ya sanya yake ci gaba da fafatawa wajen neman kujerar shugaban kasa bai wuci tsananin kishin kasar sa da ya mamaye zuciyar sa ba.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin da ziyarci wani dattijon kasa kuma jigo na jam'iyyar PDP, Cif Emmanuel Iwuanyanwu, a jihar Imo yayin da yake ci gaba da shawagin jihohin kasar nan domin tabbatar da kuma neman sahalewar kudirin sa na shugaban kasa.

Kishin Ci gaban Najeriya ya sanya nake muradin Kasancewa Shugaban 'Kasa - Atiku

Kishin Ci gaban Najeriya ya sanya nake muradin Kasancewa Shugaban 'Kasa - Atiku
Source: Depositphotos

A yayin ziyarar ta sa, tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma bayyana cewa, Najeriya ta kasance koma baya ta kowace fuska a sanadiiyar mummunan jagoranci da furucin sa yake alkantuwa da jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma jam'iyyar sa ta APC.

Turakin na Adamawa wanda tawagar sa ta hadar da shugaban yakin neman zaben sa kuma tsohon gwamnan jihar Ogun, Gbenga Daniel ya bayyana cewa, ya na manufofi gami da tsare-tsare da dama masu tarin gaske da za su magance kalubalai da kasar nan take fuskanta a halin yanzu.

KARANTA KUMA: Wani Mutum ya kashe ɗan'uwansa mara lafiya domin kaucewa biyan Kuɗin Magani

Atiku yake cewa, kishin kasa shine muhimmin jigon da ya sanya yake muradin kujerar shugaban kasa domin ciyar da Najeriya zuwa ga gaci.

Kazalika, Atiku ya kuma kalubalanci kasawar jam'iyyar APC wajen cikar burika da kuma fatan gami da sa ran da al'ummar Najeriya ta yi akan gwamnatin ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel