Tsohon sanatan PDP ya sauya sheka zuwa APC

Tsohon sanatan PDP ya sauya sheka zuwa APC

Sanata Ayogu Eze, tsohon dan majalisa kuma dan takarar gwamnan jihar Enugu karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2015 ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kafin ya koma jam’iyyar APC, Eze ya tuntunbi abokan siyasa da masu ruwa da tsaki a Enugu da kuma jam’iyya mai mulki, jaridar Daily Sun ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa an shirya wani gagarumin liyafa domin yiwa sanatan da ya riga yayi rijistan zama mamba a APC tarba na musamman.

Tsohon sanatan PDP ya sauya sheka zuwa APC

Tsohon sanatan PDP ya sauya sheka zuwa APC

An tattaro cewa mambobin jam’iyyar APC a jihar sun cika da farin ciki akan wannan ci gaba yayinda suke kallon Eze a matsayin babban runduna da zai taimaka wajen tsige PDP daga mulki a jihar a zaben 2019 mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Sauya sheka a karkashin Buhari ya banbanta da na Jonathan – Mataimatin shugaban APC

Tsohon sanatan ya tabbatar da komawarsa jam’iyyar APC mai mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel