Wata Musulma 'yar Afrika ta lashe zaben fidda gwani na majalisar wakilan Amurka

Wata Musulma 'yar Afrika ta lashe zaben fidda gwani na majalisar wakilan Amurka

Matar mai suna Ilhan Omar za ta zama 'yar takarar majalisar wakilai a zaben cike gurbi da za a gabatar a watan Nuwamban nan na bana a kasar ta Amurka

Wata Musulma 'yar Afrika ta lashe zaben fidda gwani na majalisar wakilan Amurka

Wata Musulma 'yar Afrika ta lashe zaben fidda gwani na majalisar wakilan Amurka

Wata musulma 'yar kasar Somaliya, wacce take zama a kasar Amurka, wacce a yanzu haka take matsayin 'yar majalisar jiha ta lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar Democrats domin samun damar shiga zaben majalisar wakilai da za ayi.

DUBA WANNAN: Hanyoyi guda uku da za abi don tabbatar da yiwuwar katin zabe

Matar mai suna Ilhan Omar za ta zama 'yar takarar majalisar wakilai a zaben cike gurbi da za a gabatar a watan Nuwamban nan na bana a kasar ta Amurka.

A bayanin da ta yi bayan ta lashe zaben fidda gwanin Ilhan ta ce "Muna mutukar murna da samun nasarar mu, saboda munyi iya bakin kokarin mu wurin saka jama'ar mu lokacin yakin neman zabe kuma mun yi nasara. Masu yi mana kanfen da su da 'yan sa kai sune suka karfafa mana guiwa wajen tabbatar da adalci."

Ana sa ran cewa Ilhan zata lashe zaben wanda za'ayi a wani yanki na jama'a masu son ra'ayin yanci ga kowa.

Matashiyar matar tana da shekaru 36 a duniya, inda zata zama musulma ta farko 'yar asalin Afirka da zata shiga majalisar wakilan Amurka.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel