Buhari ba ya da cikakkiyar Lafiya ta Jagorancin 'Kasar Najeriya - Tambuwal

Buhari ba ya da cikakkiyar Lafiya ta Jagorancin 'Kasar Najeriya - Tambuwal

Ta tabbata daga bakin gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayar da shaidar cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na fama kalubale na matsananciyar rashin lafiya da har ta kai sai 'yan majalisar sa ke jagorantar kasar nan.

Gwamnan na birnin Shehu ya bayyana hakan ne yayin da Matasa da dalibai suka ziyarci fadar gwamnatin sa domin bayyana godiyar su a gare sa dangane da baiwa matasa dama ta taka rawar gani cikin gwamnatin sa.

Tambuwal yake cewa, ko shakka ba bu sun goyi bayan shugaba Buhari yayin zaben 2015 sakamakon arziki na nagarta wanda a halin yanzu akwai bukatu dama da suka ɗara nagarta ta fuskar cancantar jagorancin kasar nan.

Buhari ba ya da cikakkiyar Lafiya ta Jagorancin 'Kasar Najeriya - Tambuwal

Buhari ba ya da cikakkiyar Lafiya ta Jagorancin 'Kasar Najeriya - Tambuwal

Buhari ba ya da cikakkiyar Lafiya ta Jagorancin 'Kasar Najeriya - Tambuwal

Buhari ba ya da cikakkiyar Lafiya ta Jagorancin 'Kasar Najeriya - Tambuwal

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Gwamnan ya bayyana cewa akwai ingatacciyar lafiya da kowane shugaba ke bukata domin cancantar jagorantar al'umma wanda idan aka yi dubu zuwa ga shekarar 2017 da ta gabata shugaba Buhari ya rasa wannan aminci.

KARANTA KUMA: Za a dauki Malaman Makaranta 1, 736 a jihar Jigawa

Ya ci gaba da cewa, Buhari na fama da matsananciyar rashin lafiya da ta sanya makarraban sa ke gudanar da al'amurran kasar nan da manufa ta soyuwar zukatan su kadai.

Dangane da kudirin sa na neman takarar kujerar shugaban kasa, Tambuwal ya bayyana cewa kawowa yanzu ya na ci gaba da tuntube da neman shawararin magabata akan hakan domin kuwa shugabanci wani nauyi ne da bai takaita kan mutum guda ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel