Wani dan takarar shugaban kasa ya fito da sabuwar jam'iyyar sa

Wani dan takarar shugaban kasa ya fito da sabuwar jam'iyyar sa

A jiya ne a Abuja Omoyele Sowore, shugaban shahararriyar jaridar nan ta yanar gizo 'Sahara Reporters' ya fito da wata sabuwar jam'iyya mai suna, African Action Congress (AAC)

Wani dan takarar shugaban kasa ya fito da sabuwar jam'iyyar sa

Wani dan takarar shugaban kasa ya fito da sabuwar jam'iyyar sa

A jiya ne a Abuja Omoyele Sowore, shugaban shahararriyar jaridar nan ta yanar gizo 'Sahara Reporters' ya fito da wata sabuwar jam'iyya mai suna, African Action Congress (AAC).

Sowore, wanda yake neman tikitin fitowa takarar kujerar shugaban kasa a sabuwar jam'iyyar, a halin yanzu shine shugaban jam'iyyar. Ya bayyana sabuwar jam'iyyar tare da sakataren jam'iyyar na kasa Leonard Ezenwa.

DUBA WANNAN: EL-Rufai ya gabatar da kasafin kudin 2019 ga majalisar jiha

Sowore yace sun zabi sunan jam'iyyar ne cikin salo da dabara, saboda ta zamanto a saman takardar zabe mai alamar hannaye guda biyu.

Da aka tambaye shi ko a shirye yake akan irin kalubalen dake gabanshi na fito takarar shugaban kasa, ganin yanda yake da karancin shekaru, sai yae "A shekarar 1992 na fito takarar shugaban dalibai na jami'ar jihar Lagos."

Sowore ya karya ta jita - jitar da ake yi na cewa suna nema su hade shida sauran masu neman takarar shugaban kasa, inda yace su abinda suke yi shine suga an samu hadin kai a jam'iyyu.

Sakataren jam'iyyar na kasa Dr. Ezenwa yace sun fara gabatar da taro ne a matsayin kungiya, inda daga baya suka canja suna zuwa jam'iyya, inda a yanzu haka burinsu shine su doke dukkanin manyan jam'iyyun kasar nan guda biyu wato APC da PDP.

Shugabannin jam'iyyar sun samu rakiyar Dr. Chide Nwanyawu, dan takarar gwamnan jihar Enugu a inuwar jam'iyyar ta AAC, da kuma sauran manyan jam'iyyar da matasa daga fadin kasar nan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel