Sauya sheka a karkashin Buhari ya banbanta da na Jonathan – Mataimatin shugaban APC

Sauya sheka a karkashin Buhari ya banbanta da na Jonathan – Mataimatin shugaban APC

Mataimakin shugaban jam’iyyar All Progressives Congress, Fasto Bankole Oluwajana, yace dalilan da suka sanyan yan siyasa sauya sheka a karkashin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha banban da dalilan da suka sanya su sauya sheka daga na Jonathan a 2015.

Oluwajana, wanda ya danganta manyan dalilai uku, yace yan siyasa sun bar PDP zuwa APC a 2015 saboda sun gaji da yawan rashawa da ake yi a gwamnatin Jonathan.

Ya kuma bayyana cewa yana da yakinin cewa Buhari zai yi nasara zaben 2019 duk da guguwar sauya sheka daga jam’iyya mai mulki zuwa babban jam’iyyar adawa.

Sauya sheka a karkashin Buhari ya banbanta da na Jonathan – Mataimatin shugaban APC

Sauya sheka a karkashin Buhari ya banbanta da na Jonathan – Mataimatin shugaban APC

Yace mutane sun gaji da gwamnatin PDP shiyasa duk mafi akasarin yan siyasan suka sauya sheka a waccan lokacin.

KU KARANTA KUMA: Ba na adawa da amfani da katin zabe da na’urar tantance katin zabe - Buhari

Haka zalika yace wasu rukuni na yan siyasa kuma sunyi amfani da farin jinin shugaban kasa Buhari ne domin su cimma manufarsu saboda haka bayan hakarsu ta cimma ruwa sai suka juya masa baya.

Mataimakin shugaban jam’iyyar ta APC na kasa yayi Magana ne a jihar Lagas.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel