Da dumin sa: Jami'an DSS sun cafke wani kwamishina a Najeriya

Da dumin sa: Jami'an DSS sun cafke wani kwamishina a Najeriya

Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya watau Director of Security Service (DSS) a ranar Larabar da ta gabata sun dira jihar Ebonyi dake a kudu maso gabashin Najeriya inda kuma suka cafke kwamishinan ma'aikatar tattalin arziki da samar da aikin yi na jihar.

Wannan dai na zuwa ne bayan da Kwamishinan Barista Uchenna Orji kamar a yan kwanakin nan ne ya bayyana kudurin sa na tsayawa takarar dan majalisar tarayya da zai wakilci mazabar Ivo/Ohanzara/Onicha a majalisar wakillan Najeriya.

Da dumin sa: Jami'an DSS sun cafke wani kwamishina a Najeriya

Da dumin sa: Jami'an DSS sun cafke wani kwamishina a Najeriya

KU KARANTA: Wata tsohuwa ta suma wajen ganin Atiku

Legit.ng har wa yau ta samu cewa har kawo yanzu dai ba'a san dalilin da ya sa suka cafke shi ba amma dai tuni har an nada wanda zai rike mukamin nasa a matsayin rikon kwarya.

A wani labarin kuma, Tsohon Gwamnan jihar Jigawa dake a arewacin Najeriya kuma daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), watau Alhaji Sule Lamido ya ce yaki da cin hanci da rashawar da Buhari yake yi babu gaskiya a cikin sa.

Alhaji Sule Lamido ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata a garin Lokoja babban birnin jihar Kogi a cigaba da zagayawa rangadin gaisuwa da musabaha da yakeyi da jiga-jigan jam'iyyar PDP game da zaben sa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel