Yadda cin hanci da rashawa yayi katutu a fadar shugaba Muhammadu Buhari - Wani dan takara

Yadda cin hanci da rashawa yayi katutu a fadar shugaba Muhammadu Buhari - Wani dan takara

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa dake a arewacin Najeriya kuma daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), watau Alhaji Sule Lamido ya ce yaki da cin hanci da rashawar da Buhari yake yi babu gaskiya a cikin sa.

Alhaji Sule Lamido ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata a garin Lokoja babban birnin jihar Kogi a cigaba da zagayawa rangadin gaisuwa da musabaha da yakeyi da jiga-jigan jam'iyyar PDP game da zaben sa.

Yadda cin hanci da rashawa yayi katutu a fadar shugaba Muhammadu Buhari - Wani dan takara

Yadda cin hanci da rashawa yayi katutu a fadar shugaba Muhammadu Buhari - Wani dan takara

KU KARANTA: Kasar Amurka ta rufe ofishin jakadancin ta na Abuja

Legit.ng ta samu cewa Sule Lamido yace ko kadan babu gaskiya a cikin yaki da rashawar da gwamnatin keyi domin kuwa har a fadar shugaban kasar ma cin hanci yayi katutu sannan kuma ga tsabar yunwa an kakabawa jama'ar kasa.

A wani labarin kuma, Sanatocin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP a majalisar dattawan Najeriya sun maye gurbin Sanata Akpabio da ya sauya shiga zuwa APC da Sanata Biodun Olujimi daga jihar Ekiti a matsayin shugaban marasa rinjaye.

Ita dai Sanata Biodun Olujimi ta tabayin mataimakiyar gwamnan jihar Ekiti sannan kuma kafin samun sabon mukamin nata itace mataimakiyar mai tsawatarwa a zauren na majalisar dattawa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel