Kasafin kudi: Honarabul Abdulmumin Jibrin ya yabawa Gwamnatin El-Rufai

Kasafin kudi: Honarabul Abdulmumin Jibrin ya yabawa Gwamnatin El-Rufai

Mun samu labari cewa wani ‘Dan Majalisar Jihar Kano Abdulmumin Jibrin ya yabawa wani kokari da Gwamnatin Nasir El-Rufai tayi na kammala aikin kasafin kudin shekara mai zuwa tun a watan Agusta.

Kasafin kudi: Honarabul Abdulmumin Jibrin ya yabawa Gwamnatin El-Rufai

Abdulmumin Jibrin ya yabawa aiki da cikawan Gwamnan Kaduna

Honarabul Abdulmumin Jibrin wanda ke wakiltar Mazabar Kiru da Bebeji na Jihar Kano ya jinjinawa Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasir El-Rufai da ta mikawa Majalisa kundin kasafin kudin 2019 tun yanzu.

Jibrin yayi amfani da shafin sa na Tuwita ne ya yabi Gwamnatin Kaduna inda ya nemi Gwamnatin Najeriya ta dauki darasi wajen Gwamna El-Rufai. Sai kwanan nan ne dai aka amince da kasafin kudin Gwamnatin Tarayya na 2018.

KU KARANTA: Satar inna-naha da ake yi a Gwamnatin Buhari ya sa ake cin bashi – PDP

Hon. Jibrin yace Gwamnan Kaduna ya nunawa Duniya cewa ba abu bane da ba zai yiwu ba na ace an kammala aikin kasafin kudin Gwamnati da wuri haka. Jibrin yayi kira da sauran Gwamnatocin Jihohi da su yi koyi da Jihar Kaduna.

Kusan dai ba a taba ganin an kammala aikin kasafin kudin shekara mai zuwa da wuri haka a kasar nan ba. Yanzu dai har Gwamnatin Jihar Kaduna ta mikawa Majalisar dokoki kundin kasafin 2019 domin a tabbatar da shi a jira lokacin aiki yayi.

Jama’a dai sun jinjinawa aiki da cikawan Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai wanda ya ware Ma’aikata sun-ku-tu-kum domin aikin kasafim kudi da tsare-tsare. Wani Matashi Muhammad Sani Dattijo ne kwamishinan wannan aiki a Jihar ta Kaduna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel