Ya kamata Buhari ya kori mutanen banzan da ke tare da shi - Inji Ogbemudia Jr.

Ya kamata Buhari ya kori mutanen banzan da ke tare da shi - Inji Ogbemudia Jr.

Babban ‘Dan Marigayi Samuel Ogbemudia ya bayyana cewa akwai wasu mutanen da ba na-kwarai a cikin Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wadanda ke shirya masa zagon-kasa ko ta ina.

Ya kamata Buhari ya kori mutanen banzan da ke tare da shi - Inji Ogbemudia Jr.

Ana zargin cewa mutanen banza sun zagaye Shugaba Buhari

Samuel Ogbemudia Jr. wanda shi ne babban ‘Dan Marigayi tsohon Gwamnan Bendel a lokacin Soji ya bayyanawa ‘Yan Jarida cewa akwai wasu manyan mukarrabai a Gwamnatin Tarayya da Jihohin kasar nan da su ke hana ruwa guda.

KU KARANTA: Tsohon Dogarin Abacha na neman tsayawa takara a 2019

Ogbemudia Jr. yake cewa wasu bata-gari su na nan a cikin Gwamnati don haka zai yi wahala ‘Yan Najeriya su dandana romon wannan Gwamnati. Ogbemudia ya nemi Shugaban kasar ya kori duk masu kawo masa matsala a kusa da-shi.

Wannan Bawan Allah da yake bayani a Garin Benin da ke Jihar Edo yace har sai lokacin da Shugaba Buhari ya haska ya gano bata-garin da ke zagaye da shi ne a a samu zaman lafiya a kuma ji dadin kokarin da Gwamnatin sa ta ke yi.

Vanguards ta kuma rahoto cewa Samuel Ogbemudia Jr. ya nemi mutanen Kudancin Jihar Edo su zabi wanda zai kare mutuncin su da martabar su a Majalisar Tarayyar Kasar a zabe mai uwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel