Muna shan ɗan-karan tambaya daga hannun jami’an hukumar EFCC – Inji Gwamna Samuel Ortom

Muna shan ɗan-karan tambaya daga hannun jami’an hukumar EFCC – Inji Gwamna Samuel Ortom

Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom ya bayyana cewa hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa ta’annuti, EFCC, tana matsa masa tare da manyan jami’an gwamnatinsa babu gaira babu dalili, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Gwmanan yana cewa takurar da hukumar EFCC ke yi masa da jami’an gwmanatinsa ya yi yawa, har ma ya zama tamkar wani wasan kwaikwayo abin dariya.

KU KARANTA: Tura ta kai bango: Anyi artabu tsakanin jama’an gari da yan ta’addan jihar Zamfara

Kaakakin Gwamna Ortom, Terver Akase ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, 15 ga watan Agusta, inda yace babu wata rana da zata zo ta wuce ba tare da EFCC ta bullo da wata sabuwar cin mutunci ga wani jami’in gwamnatin ba.

Mun sha ɗan-karan tambaya daga hannun jami’an hukumar EFCC – Inji Gwamna Samuel Ortom

Gwamna Samuel Ortom

“A yanzu EFCC ta bullo da wani sabon salo, wai tana bukatar gwamnatin jihar Benuwe ta mika mata takardun dake kunshe da dukkanin bayanan da majalisar tsaro ta jihar ke tattaunawa a yayin zamanya, na kowani mako.” Inji Tever.

Sai dai Kaakakin ya kalubalanci wannan bukata ta EFCC, inda yayi tambaya: “Shin aikin hukumar ya shafi kula tare da sa ido akan lamarin tsaron jaha ne?” saboda a cewarsa idan haka ne ya kamata EFCC ta nemi bayanan shugaban kasa da na sauran gwamnoni.

Har ila yau akwai wasu yan majalisun dokokin jihar Benuwe dake hannun hukumar EFCC, inda suke shan tambayoyi dangane da wata bahallatsar cinikin sayan motoci tun farkon wannan gwamnatin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel