EL-Rufai ya gabatar da kasafin kudin 2019 ga majalisar jiha

EL-Rufai ya gabatar da kasafin kudin 2019 ga majalisar jiha

A jiya ne gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i, ya gabatar da kasafin jihar na shekarar 2019 ga majalisar jihar, kudin da yakai naira biliyan 155.8

EL-Rufai ya gabatar da kasafin kudin 2019 ga majalisar jiha

EL-Rufai ya gabatar da kasafin kudin 2019 ga majalisar jiha

A jiya ne gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i, ya gabatar da kasafin jihar na shekarar 2019 ga majalisar jihar, kudin da yakai naira biliyan 155.8.

A cikin kasafin kudin, wanda aka raba shi kashi biyu, kashi na farko an ware naira biliyan 62.339 domin gabatar da ayyuka irin na yau da kullum, sannan kashi na biyu an ware naira biliyan 93.526 domin manyan ayyuka.

DUBA WANNAN: Hanyoyi guda uku da za abi don tabbatar da yiwuwar katin zabe

A wannan shekarar da muke ciki, gwamnan ya fitar d kasafin naira biliyan 216.65, inda aka samu ragin kashi 28 cikin dari a shekarar 2019.

Gwamnan yayi alkawarin kammala dukkanin ayyukan da ya fara a dukkanin kananan hukumomi 23 da ke fadin jihar.

A lokacin da yake gabatar da kasafin, gwamnan yace gwamnatin sa zata yi kokari wurin ganin ta baiwa talakawa da 'ya'yansu ingantacciyar rayuwa.

Shugaban majalisar jihar Aminu Shagali yace, majalisar taji dadin hanyoyin da gwamnatin jihar ta bi domin gabatar da kasafin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel