Takkadama: Kan Sanatocin APC ya rabu a kan maye gurbin Saraki

Takkadama: Kan Sanatocin APC ya rabu a kan maye gurbin Saraki

Rahotan da muka samu daga Daily Trust na nuna cewa an samau baraka tsakanin Sanatocin jam'iyyar APC a kan batun maye gurbin shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki.

Wasu daga cikin Sanatocin na ganin Sanata Ahmad Lawan (APC, Yobe) ne yafi dacewa ya maye gurbin yayin da wasu kuma sun dage cewa Sanata Godswill Akpabio (Akwa Ibom) ne yafi cancanta da kujerar.

Wata majiya ruwaito cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole yace kan 'yan jam'iyyar ya rabu gida biyu a taron kwamitin masu ruwa da tsaki a jam'iyyar da aka yi a ranar Talata.

Kan Sanatocin APC ya rabu a kan magajin Saraki

Kan Sanatocin APC ya rabu a kan magajin Saraki

Majiyar Legit.ng ta gano cewa a taron da akayi a baya, an zabi Lawan a matsayin wanda zai maye gurbin Saraki da Sunny Ogbuoji (APC, Ebonyi) a matsayin mataimakinsa wanda zai maye gurbin mataimakin shugaban majalisa, Ike Ekweremadu.

DUBA WANNAN: Buratai da wasu manyan Soji 49 sun rubuta wata muhimmiyar jarabawa a hedkwatan Soji dake Abuja

A gudanar da taron na ranar Talata ne cikin sirri a Sheraton Hotel dake Abuja.

Wani dan majalisa ya ce an kira taron ne saboda a duba yadda za'a warware rashin jituwar da ke tsakanin 'yan majalisar tarayya da gwamnonin jiha amma an daga baya akallar taron ya karkata ga yadda za'a canja shugabanin majalisar dattawa.

Wasu sanatoci biyu daga yankin Arewa maso yamma sun bayyana yadda suka fuskanci ukuba a hannun gwamnonin jiharsu.

Daya daga cikinsu ya ce asalin dalilin da ya janyo rashin jituwa tsakaninsa da gwamnan jiharsa shine marawa Lawan baya da ya yi a zaben shugabanin majalisa.

An kuma tattauna game da halin da Sanata Babajide Omoworare da Soji Akanbi da Yahaya Abdullahi suke ciki.

"Wani Sanata ya ce Saraki yana musgunawa Sanatocin uku ne saboda sun goyi bayan Lawan. Amma abin takaici shine bayan Lawan ya zama shugaban majalisa, bai tabbuka komai ba don magance matsalar," inji majiyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel