Matsalar tsaro: Na gamsu da kamun ludayin shugaba Buhari – Abdul Aziz Yari

Matsalar tsaro: Na gamsu da kamun ludayin shugaba Buhari – Abdul Aziz Yari

Gwamnan jihar Zamfara Abdul Aziz Yari ya bayyana cewa kokarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari keyi game da kawar da matsalar tsaro daya addabi jihar Zamfara, kwalliya ta fara biyan kudin sabulu.

Legit.ng ta ruwaito Yari ya bayyana haka ne a gaban mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo wanda ya kai ziyarar aiki na kwana daya jihar Zamfara a ranar Laraba 15 ga watan Agusta, inda yace zaman lafiyar da ake samu zai samar da cigaba mai daurewa a jihar.

KU KARANTA: Tura ta kai bango: Anyi artabu tsakanin jama’an gari da yan ta’addan jihar Zamfara

Matsalar tsaro: Na gamsu da kamun ludayin shugaba Buhari – Abdul Aziz Yari

Osinbajo da Abdul Aziz Yari

“Sakamakon matsalar tsaro da muke ta fama da shi a jihar Zamfara, gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhamamdu Buhari na bamu dukkan gudunmuwar da muka nema a kowanni lokaci.” Inji Gwamna Abdul Aziz Yari.

A nasa jawabin, mukaddashin shugaba Osinbajo yace: “Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zata ja da baya ba wajen maganc dukkanin matsalolin tsaro dake damun wani sashi na Najeriya, bama Zamfara kadai ba.”

Matsalar tsaro: Na gamsu da kamun ludayin shugaba Buhari – Abdul Aziz Yari

Ziyarar

Haka zalika gwamnan ya zagaya da Osinbajo zuwa wasu manyan ayyuka a jihar don ya kaddamar dasu da suka hada da Tituna, ruwan sha, sabbin makarantu da Asibitoci da ma wadanda gwamnatinsa ya gyara.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel