Barazanar fatattakar Najeriya daga FIFA: Osinbajo ya garkame kofa da Ministan wasanni

Barazanar fatattakar Najeriya daga FIFA: Osinbajo ya garkame kofa da Ministan wasanni

Mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya kulle kofa da ministan harkokin wasanni da al’amuran matasa, Barista Solomon Dalung inda suka tattauna batun daya shafi barazanar fatattakar Najeriya daga harkar kwallon kafa wanda hukumar FIFA ta yi.

Daily Trust ta ruwaito Osinbajo ya yi wannan ganawar sirri da Minista Dalung ne jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa na ranar Laraba, 15 ga watan Agusta, a fadar shugaban kasa dake babban birin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Tura ta kai bango: Anyi artabu tsakanin jama’an gari da yan ta’addan jihar Zamfara

Ana ta fama dauki ba dadi tsakanin shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya-NFF, Amaju Pinnick da dan takarar kujerar shugaban hukumar, Chris Giwa wanda yayi ikirarin wata Kotu ta bashi shugabancin hukumar, wanda hakan ya sa a yanzu haka jami’an tsaro na DSS suka mamaye ofishin hukumar.

Barazanar fatattakar Najeriya daga FIFA: Osinbajo ya garkame kofa da Ministan wasanni

Osinbajo da Dalung

Sai dai hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA dake daure ma Amaju gindi ta umarci gwamnatin Najeriya data daina shiga harkar NFF, kuma ta tabbata kafin ranar Litinin mai zuwa ta mayar da ragamar shugabancin NFF ga Amaju.

Da wannan ne FIFA tace idan har Najeriya bata bi wannan umarni nata ba, tabbas zata hukunta kasar ta hanyar fatattakarta daga kungiya, tare da hanata shiga duk wani harkar kwallon kafaa Duniya gaba daya.

Bugu da kari majiyar Legit.ng ta ruwaito kafin a fara zaman taron majalisar zartarwa na ranar Larabar, shima Amaju Pinnick ya yi wata ganawar sirri tsakaninsa da mukaddashin shugaban kasa Osinbajo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel