Buratai da wasu manyan Soji 49 sun rubuta wata muhimmiyar jarabawa a hedkwatan Soji dake Abuja

Buratai da wasu manyan Soji 49 sun rubuta wata muhimmiyar jarabawa a hedkwatan Soji dake Abuja

Babban hafshin sojin kasa, Laftanat Tukur Buratai tare da wasu manyan jami'an sojoji 49 sunyi wata jarabawa ta musamman a ranar Laraba a hedkwatan Soji dake Abuja inda suka gwada kwarewarsu a manyan harsunan Najeriya uku wata Hausa, Yarabanci da Ibo.

Kakakin hukumar Sojin Najeriya, Texas Chukwu, yace wannan gwajin da akayi musu yana daya daga cikin yunkurin da hukumar keyi don ganin dukkan jami'anta sun kware wajen magana da manyan harsunan Najeriya guda uku.

Mr Chukwu, ya ce an shiya musu jarabawar ce bayan sun kwashe watanni takwas daukan darasa babu kama hannun yaro wanda hedkwatan hukumar sojin dake Abuja ta shirya saboda manyan jami'anta.

Buratai da wasu manyan soji 49 sun rubuta wata muhimmiyar jarabawa a hedkwatan soji dake Abuja

Buratai da wasu manyan soji 49 sun rubuta wata muhimmiyar jarabawa a hedkwatan soji dake Abuja

DUBA WANNAN: Asha: 'Yan bindiga sun kashe tsohon mataimakin shuganban NPS a gonarsa

Ya ce hukumar sojin tayi imani cewa fahimtar wadannan manyan harsunan guda uku zai taimaka matuka wajen gudanar da ayyukan samar da tsaro a sassan kasar nan.

"Wannan sabon tsarin kuma zai kara kawo hadin kai da tsakanin jami'an sojin da jama'a."

Mr Chukwu ya ce wadanda suka rubuta jarabawar sun hada da Manyan shugabanin dake hedkwatan hukumar soji, Kwamandojin runduna, Direktoci da wasu manyan jami'an.

Kakakin hukumar ya ruwaito cewa Mr Buratai ya yabawa jami'an sojin da suka rubuta jarabawar kan yadda suka bayar da hadin kai.

Shugaban hukumar sojin yace za'a fitar da sakamakon jarabawar mako mai zuwa kana zasu sake rubuta wata jarabawar mako mai zuwa.

Tun lokacin da Buratai ya kama aiki a matsayin shugaban soji a shekarar 2015, ya bukaci jami'an soji su bayar da himma wajen koyan manyan harsunan Najeriya sobada inganta aiki tsakanin sojin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel