Zaben 2019: Za’a ciyar da yan sanda da kudi N6bn kacal

Zaben 2019: Za’a ciyar da yan sanda da kudi N6bn kacal

Yayin gudanar da zaben 2019, hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC za ta ciyar da yan sandan da zatayi amfani da su wajen zabe da kudi naira biliyan shida.

Wannan na kunshe cikin kasafin kudin da hukumar INEC ta mikawa majalisar wakilai a ganawarsu ta yau.

Yan majalisan sun tada jijiyoyin wuya kan wadannan bukatu da shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya gabatar.

NAIJ.com sun kawo muku rahoton cewa Kwamitin majalisar wakilan tarayya kan harkokin gudanar da zaben sun shiga ganawa da jami’an hukumar gudanar da zabe ta asa mai zaman kanta wato INEC da safen nan a zauren majalisa.

KU KARANAT: ‘Yan sanda sun yi namijin kokorin kama ‘yan bindiga 20 da makamai masu yawa a Zamfara

Shugaban hukumar INEC, farfesa Mahmoud Yakubu, ne ya jagoranci sauran jami’an hukumar domin muqabala kan bukatan kudin da suk mika na gudanar da zaben 2019.

Kwamitin karkashin jagorancin Mrs Aisha Dukku zasu yi tambayoyi don tabbatar da gaskiyan abubuwan a hukumar INEC ta bukaci yi da kudi sama da Biliyan N240bn.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel