Da zaman banza: Wani fursuna da aka yankewa hukuncin kisa ya fara karatun digiri na biyu

Da zaman banza: Wani fursuna da aka yankewa hukuncin kisa ya fara karatun digiri na biyu

Wani fursuna, Jude Onwuzulike dake gidan yari ta garin Awka dake jihar Anamba ya koma fara karatun digiri na biyu a fannin ilimin sarrafa bayanai ta hanyar amfani da fasahar zamani (IT) a jami’ar kasa ta kowa da kowa (NOUN).

A ranar Litinin ne Jude mai shekaru 39 da ‘ya’ya 4 ya shiga ayarin ragowar daliban da jami’ar tayi bikin karbar su domin fara karatu a zangon shekarar 2018/2018 da aka yi a harabar gidan yarin ta Awka.

Da yake zantawa dfa manema labarai, Jude, ya bayyana cewar yana da yakinin cewar iliminsa zai yi masa amfani wataran.

Da zaman banza: Wani fursuna da aka yankewa hukuncin kisa ya fara karatun digiri na biyu

Fursuna Jude da jami'an kula da gidan yari da wakilan jami'ar NOUN

Ya kara da cewar tun kafin ya gamu da tsautsayin day a kawo shi gidan yarin ya yi karatun digiri na farko da babbar difloma a jami’ar Najeriya ta Nsukka.

DUBA WANNAN: Manyan 'yan takarar shugaban kasa 5 da suka ziyarci Obasanjo kwanan nan

A shekarar 2005 na kamala digirina na farko a bangaren ilimin akawu yayin da nayi babbar difloma a bangaren lissafi. Bayan na zo giudan yari nayi wata diflomar a bangaren IT kuma gas hi yanzu zan yi digiri na biyu a bangaren,” a cewar Jude.

A jawabinsa, shugaban jami’ar NOUN, Farfesa Abdallah Uba Adamu, wanda Dakta Scholastica Ezeribe ya wakilta, ya bayyana jin dadinsa bisa karfin halin da Jude day a nuna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel