Dalilin da yasa muke bukatar N189bn domin zaben 2019 - INEC

Dalilin da yasa muke bukatar N189bn domin zaben 2019 - INEC

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta INEC, Mahmood Yakubu, ya bayyana dalilan da yasa hukumar tayi kari kan kasafin kudin gudanar da babban zaben shekarar 2019.

Ya yi wannan bayanin ne a ranar Laraba yayin da yake gabatarwa 'yan mambobin kwamitin zabe na majalisar tsare-tsaren zaben shekarar ta 2019 a babban birnin tarayya Abuja kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Dalilan da ya bayar sun hada da karin adadin jam'iyyun zabe, karin adadin masu kada kuri'a da masu rajista, tsadar sufuri, hauhawar dallar a kasuwar canji, da karin yawan mazabun zabe.

Dalilan da yasa muke bukatar N189.2bn domin gudanar da zaben 2019 - INEC

Dalilan da yasa muke bukatar N189.2bn domin gudanar da zaben 2019 - INEC

Hukumar ta INEC tayi amfani da N120 biliyan wajen gudanar da zaben shekarar 2015 amma a wannan shekarar ta bukaci a ware mata N189.2 biliyan domin zaben shekarar 2015.

DUBA WANNAN: Abun kunya: An yi baran-baran tsakanin shugabannin PDP a wata jiha saboda ziyarar Atiku

Wannan ya nuna cewa an samu karin N69 biliyan akan kudin da akayi amfani dashi wajen gudanar da zaben shekarar 2015.

Shugaban na INEC yace a yanzu adadin jam'iyyun siyasa sun kai 91 a maimakon jam'iyyu 44 da hudu da ake dasu a shekarar 2015.

Yace karin adadin jam'iyyun zaben zai shafi girmar takada da kudin da za'a kashe wajen buga takardan zaben.

Mr Yakubu ya kuma ce hauhawar farashin kayayakin man fetur da hauhawar kudaden kasashen waje a kasuwar canji suma suna daga cikin dalilan da yasa kasafin kudin hukumar ta karu.

"Muna bukatan bude sabin rumfunan zabe, zamu kara adadin ma'aikatan wucin gadi da zamu dauka, masu sanya idanu a zabe da baturen zabe, inji Mahmud.

Ya kara da cewa a ranar 11 ga watan Augusta, hukumar ta yiwa mutane 12.1 miliyan rajistan zabe.

A wasikar da ya aikewa majalisar, shugaba Muhammadu Buhari ya yi umurni ba bawa INEC N143.5 biliyan a wannan shekarar sannan a basu ragowar N45.6 biliyan a shekarar 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel