Zamu bijrewa duk wani yunkuri na tsige Saraki - Dan majalisa

Zamu bijrewa duk wani yunkuri na tsige Saraki - Dan majalisa

- Sanata Philip Gyunka yace duk wata ba zasu amince da duk wata makarkashiya da ake shiryawa na tsige Saraki ba muddin ta sabawa doka

- Yace Sanatocin PDP sun sanya idanu suna lura da duk wata yunkuri da za'ayi domin cimma wannan manufar

- Gyunka ya gargadi shugaban APC, Adams Oshiomhole, cewa batun tsige shugaban majalisa ta banbanta da gwagwarmayar kungiyoyi da ya saba yi a baya

A yau Laraba ne 15 ga watan Auguta ne dan majalisar tarayya, Sanata Philip Gyunka, ya ce ba zasu amince da duk wata makarkashiya da ake shiryawa na tsige Saraki ba muddin ta sabawa kundin tsarin mulki.

Gyunka mai wakiltan mazabar Nasarawa ta Arewa a jihar Nasarawa ya furta wannan magana ne a taron yakin neman zabensa inda ya bayyana niyyarsa na fitowa takarar gwamnan a jihar kamar yadda NAN ta ruwaito.

Ba zamu amince da wata yunkuri na tsige Saraki ba bisa ka'ida ba - 'Yan Majalisar PDP

Ba zamu amince da wata yunkuri na tsige Saraki ba bisa ka'ida ba - 'Yan Majalisar PDP

Legit.ng ta gano cewa Gyunka, ya nuna damuwarsa kan yadda shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomhole, ke katsalandan cikin lamarin da tuni kundin tsarin mulkin Najeriya ta fayyace wanda ya kamata ya zama shugaban majalisar dattawa.

DUBA WANNAN: Bayan kai ruwa rana a baya, yanzu Kwankwaso zai ziyarci Kano

A cewarsa, kundin tsarin mulkin ta baiwa kowane dan majalisa ikon zama shugaban majalisa ba kamar mukamin shugaban masu rinjaye da marasa rinjaye ba wanda dole su kasance daga jam'iyyar dake rinjaye ko akasin hakan.

Ya kuma ce akwai ka'idoji da doka ta shimfida kan yadda 'yan majalisar zasu iya tsige duk shugaban da basu gamsu da irin kamun ludayinsa ba.

"Doka ta fadi karara cewa duk lokacin da kashi biyu cikin uku na 'yan majalisar suka nuna rashin gamsuwarsu da shugaba, toh babu makawa zasu iya tsige shi.

"Hakan yasa nake mamakin yadda Oshiomhole ke barazanar cewa dole sai an tsige Saraki duk da cewa shi ba dan majalisa bane." inji Gyunka.

Yace Sanatocin PDP sun sanya idanu suna lura da duk wata yunkuri da za'ayi domin cimma wannan manufar tsige Saraki ba bisa ka'ida ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel