2019: Manyan yan takarar kujerar shugaban kasa 4 da suka ziyarci Obasanjo kwanan nan

2019: Manyan yan takarar kujerar shugaban kasa 4 da suka ziyarci Obasanjo kwanan nan

Yayinda guguwar zaben 2019 ke dada matsowa kusa, manyan yan takarar kujerar shugaban kasa na fafutukar neman goyon bayan masu ruwa da tsaki a fadin kasar.

A yan kwanakin nan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo na ta samun baki dake kai masa ziyara.

Oasanjo dai ya mulki kasar nan tsawon shekaru 12, yayi shekaru 4 na farko a matsayin shugabna kasa a mulkin soja sannan yayi shekaru 8 a matsayin shugaban kasar damokradiya.

2019: Manyan yan takarar kujerar shugaban kasa 4 da suka ziyarci Obasanjo kwanan nan

2019: Manyan yan takarar kujerar shugaban kasa 4 da suka ziyarci Obasanjo kwanan nan

Ga wasu daga cikin manyan yan takarar shugaban kasa da suka ziyarce shi:

1. Atiku Abubakar:

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya wadda suka dade da raba gari da Obasanjo, sai dai a kwanan ne aka hange shi tare da tsohon ubangidan nasa.

Jigon na PDP ya dade da nuna kudirinsa na son takarar kujerar shugaban kasa a Abuja. An gano shi tare da Obasanjo a ranar 27 ga watan Yuli a wajen wani taro.

2. Sule Lamido:

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi ganawar sirri da tsohon shugaban kasar tsawon sa’o’i biyu a dakin litattafansa dake Abeokuta, inda yake neman goyon bayansa.

3. Bukola Saraki

Bayan sauya shekarsa daga jam’iyya mai mulki zuwa PDP, shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya ziyarci Obasanjo a dakin karatunsa a ranar 14 ga watan Agusta.

Shima dai ana rade-radin cewa yana neman kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

4. Ibrahim Dankwambo:

Haka zalika Ibrahim Dankwambo, gwamnan jihar Gombe kuma dan takarar kujerar shugaban kasa zabe mai zuwa ya gana da Obasanjo a Abeokuta, jihar Ogun a ranar Talata, 14 ga watan Agusta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel