‘Yan sanda sun yi namijin kokorin kama ‘yan bindiga 20 da makamai masu yawa a Zamfara

‘Yan sanda sun yi namijin kokorin kama ‘yan bindiga 20 da makamai masu yawa a Zamfara

- Jami'an tsaro sun samu gagarumar na kan 'yan ta'addan da suke addabar jihar Zamfara

- 'Yan sandan sun kuma kama makamai da yawa a tare da 'yan bindgar

Rundunar ‘yan Sandan jihar Zamfara sun samu nasara kan wasu ‘yan bindiga guda 20, mutanen an same su ne dauke da miyagun makamai ciki har da bindigogi kirar AK 47 guda bakwai.

Da kyau: ‘Yan sanda sun yi namijin kokorin kama ‘yan bindiga 20 da makamai masu yawa a Zamfara

Da kyau: ‘Yan sanda sun yi namijin kokorin kama ‘yan bindiga 20 da makamai masu yawa a Zamfara

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Zamfara Kenneth Ebrimson ne ya bayyana hakan a yau a lokacin da yake wa manema labarai karin haske.

Ebrimson ya bayyana cewa jami'an ‘yan sanda na musamman masu yaki da ‘yan fashi da makami wadanda suke karkashin Sufeton ‘yan sanda na kasa, sune suka samu nasarar cafke ‘yan bindigar.

KU KARANTA: An rasa Jami'an Tsaro 30 cikin wata guda a Najeriya - Kwamishinan 'Yan sanda

“Ba zamu fadi yadda muka yi nasarar kama wadannan ‘yan bindigar ba, kuma ba zamu fadi sunayensu ba bisa dalilai na tsaro".

“Bisa matakan da muka dauka, hakan yana bamu karfin gwiwar cewar dama zamu samu nasarar damke wadannan ‘yan bindigar".

A karshe kwamishinan kuma ya ce rundunar ‘yan sandan ta kaddamar da wani shiri mai taken kawar da tsoro da jitata a tsakankanin al'ummar ta jihar Zamfara.

Ya kuma Shawarci mazauna jihar da su dinga sanar da jami'an tsaron dukkanin wani abu da su amince da shi ba domin magance matsalar tsaron da jihar take fama da shi.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel