An matsa min lamba na fito takarar shugaban kasa - Gwamna Tambuwal

An matsa min lamba na fito takarar shugaban kasa - Gwamna Tambuwal

A yau Laraba ne gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato ya bayyana cewa an yana fuskantar matsin lamba domin fitowa takarar shugabancin kasa a zaben 2019.

Tambuwal ya furta hakan ne lokacin da yake jawabi ga wasu kungiyoyin matasa, dalibai da jama'ar jihar Sakkwato da suka kai masa ziyara a fadar gwamnati.

A cewarsa, "Ina ta samun shawarwari da kalaman goyon baya daga shugabanin mu da mutane da dama daga sassa daban na Najeriya har ma da kasashen waje inda suke nema in fito takara kuma yanzu kiraye-kirayen ya yi karfi".

An matsa min lamba na fito takarar shugaban kasa

An matsa min lamba na fito takarar shugaban kasa

Tambuwal ya yi bayyani cewa ba yinsa bane sai dai irin matsin lamba da yake fuskanta daga wurare da yawa tare da matsalar shugabanci da ake fama dashi a kasar.

DUBA WANNAN: Zamu maka Najeriya a duhu - Ma'aikatan lantarki sun yi barazanar yajin aiki

Ya ce zai sanar da jama'a matsayarsa a cikin 'yan kwanki masu zuwa.

A bangarensa, jagoran kungiyoyin, Kwamared Bashir Gorau, ya yi alkawarin bawa gwamna Tambuwa goyon baya muddin ya amince ya fito takarar shugabancin kasar.

"Mun gaji da jira, muna son ka bayyana mana matsayarka yanzu," inji shi.

A wata rahoton, Legit.ng ta kawo cewa wata jigo a tafiyar Kwankwasiya, Hajiya Binta Sifikin ta yi magana a kan shigowar Sanata Kwankwaso Kano a karo na farko tun bayan canjin shekar sa daga jam’iyyar APC zuwa tsohuwar jam’iyyar sa ta PDP.

A cewar Hajiya Binta Sifikin, “tabbas Sanata Kwankwaso zai shigo Kano idan lokaci ya yi kuma babu abibda zai iya dakatar da shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel