Manyan mutane a Najeriya sun nemi ‘Yan Sanda su saki ‘Dan jaridar da aka damke

Manyan mutane a Najeriya sun nemi ‘Yan Sanda su saki ‘Dan jaridar da aka damke

Mu na samun labari cewa jama’a sun fito sun yi ca a kan ‘Yan Sandan Najeriya inda su ka nemi a saki wani ‘Dan jaridar Premium Times da yake tsare hannun Jami’an tsaro babu gaira babu dalili tun Ranar Talata.

Manyan mutane a Najeriya sun nemi ‘Yan Sanda su saki ‘Dan jaridar da aka damke

Ana neman 'Yan Sanda su saki Samuel Ogunipe da aka tsare

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar yayi kira ga ‘Yan Sandan Najeriya yana fada masu cewa tsare Samuel Ogunipe da ake yi ya sabawa tsarin mulkin kasa kuma an keta masa alfarma. Atiku ya nemi ayi maza a saki wannan Bawan Allah.

KU KARANTA: ‘Dan jaridar ds DSS su ka rufe tun a 2016 yace yana cikin wani hali

Sanatan Jihar Kaduna ta tsakiya watau Kwamared Shehu Sani ya nemi ‘Yan Sandan kasar su kyale wannan Bawan Allah da yanzu ya kwana a hannun su. Kwamared Shehu Sani yace dole a bar ‘Yan jarida su yi aikin su babu tsangwama a kasar nan.

Tun jiya ne Jami’an tsaro na SARS su ka kama Samuel Ogundipe da wasu Abokan aikin sa 2; Musikilu Mojeed da Azeezat Adedigba. Mun samu labari cewa duk an sake sauran sai dai har yanzu Ogundipe na hannun ‘Yan Sandan na Najeriya a garkame.

Ku na da labari cewa Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya nemi Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya Ibrahim K. Idris yayi wa Jami’an tsaro na SARS garambawul. Ana yawan zargin SARS da cin zarafin jama’a ba tare da hakki ba a cikin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel