Sanatocin APC sun ci al washi tare da kammala shirin tsige Saraki

Sanatocin APC sun ci al washi tare da kammala shirin tsige Saraki

Shirin Sanatocin jam’iyyar APC na tsige shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya kara karfi bayan wata ganawa tsakanin ‘yan majalisar ta dattijai da shugabancin jam’iyyar APC.

Yayin wata ganawar tasu a jiya da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams oshiomhole, sanatocin APC sun bayyana cewar zasu yi amfani da yawansu domin cimma kudirinsu na tsige Saraki tare da tursasa majalisar dawowa daga hutun da ta tafi.

Oshiomhole ya godewa mambobin majalisar bisa biyayyar su ga APC tare da shaida masu cewar da adadin ‘yan majalisar wakilai 196 da sanatoci 56 da jam’iyyar ke da su babu abinda zai hana su canja shugabacin majalisa.

Sanatocin APC sun ci al washi tare da kammala shirin tsige Saraki

Sanatocin APC

Shugaban jam’iyyar ya yi watsi da zargin cewar gwamnatin shugaba Buhari na da hannu a shinge kofar shiga majalisa da jami’an hukumar tsaro ta DSS suka yi a satin da ya gabata.

Kazalika ya yi watsi da rahotannin cewar ya jagoranci wani taro da sanatocin jam’iyyar ta APC a gidansa a daren ranar Litinin.

DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa tayi karin haske a kan rahoton karin wa'adin hutun Buhari

Duk masu ganin bai kamata a tsige Saraki ba zasu iya tafiya duk kotun da suka ga dama bayan an tsige shi domin neman sanin ko yin hakan ya sabawa doka.

Muddin ka rasa rinjaye a majalisa yin murabus ne kadai zai hana a tsige ka, a saboda haka idan baya son a tsige shi zai iya barin kujerar sat a hanyar girma da arziki,” a cewar Oshiomhole.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel