Wani Mutum ya kashe ɗan'uwansa mara lafiya domin kaucewa biyan Kuɗin Magani

Wani Mutum ya kashe ɗan'uwansa mara lafiya domin kaucewa biyan Kuɗin Magani

A yayin da lamarin duniya a kullum yake kara sabuntawa mun samu rahoton cewa, wani Mutum mai shekaru 40 a duniya ya salwantar da rayuwar ɗan'uwansa marar lafiya domin gujewa fitar da kudin sa wajen nema masa lafiya.

Rahoton dai kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito ya bayyana cewa, lamarin mai cike da ban mamaki gami da al'ajabi ya auku ne a kauyen Ugwuabo na karamar hukumar Igbe-Eze ta Arewa dake can jihar Enugu.

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, SP Ebere Amaraizu, shine ya tabbatar da aukuwar lamari yayin ganawa da manema labarai cikin birnin Enugu a ranar Laraba ta yau din nan.

Binciken hukumar 'yan sandan ya tabbatar da cewa wani Mutum mai shekaru 40 a duniya, Raphael Izuchukwu, ya kashe ɗan'uwansa, Chizoba Ogbonna mai shekaru 46 a duniya tare da haka rami da binne gawarsa.

Wani Mutum ya kashe ɗan'uwansa mara lafiya domin kaucewa biyan Kuɗin Magani

Wani Mutum ya kashe ɗan'uwansa mara lafiya domin kaucewa biyan Kuɗin Magani

A yayin ci gaba da tsananta bincike, hukumar 'yan sandan ta gano cewa Raphael ya kashe ɗan'uwansa ne sakamakon rashin lafiya da yake fama da ita wanda shi kuma ya gaza wajen ci gaba da biyan kudin magani na jinyar sa.

KARANTA KUMA: Dogara ya bayyana Matsalar dake kawo naƙasun Cigaban harkokin wasanni a Najeriya

Kungiyar leken asiri reshen hukumar 'yan sanda ta bankado cewa, bayan raba ɗan'uwansa da rayuwar duniya, Raphael ya kuma haka rami inda ya binne gawar sa domin ya huta da dawainiya.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, gwamnatin jihar Jigawa dake Arewacin Najeriya za ta dauki ma'aikata 1, 736 domin koyar da dalibai a makarantun Firamare da Sakandire sakamakon karanci da suka yi a fadin jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel