Abun kunya: An yi baran-baran tsakanin shugabannin PDP a wata jiha saboda ziyarar Atiku

Abun kunya: An yi baran-baran tsakanin shugabannin PDP a wata jiha saboda ziyarar Atiku

A jiya Laraba ne rikici ta barke tsakanin wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP ciki har da mataimakin kakakin majalisar wakilai na kasa, Cif Emeka Ihedioha, tsohon ministan jiragen sama, Kema Chikwe, dan majalisar wakilai, Jones Onyeriri da wasu a ofishin mamban kwamitin amintattun na PDP, Cif Emmanuel Iwuanyanwu saboda ziyarar da Atiku Abubakar ya kai jihar Imo.

Jiga-jigan jam'iyyar PDP da suka hallarci taron da akayi a glass house sun fusatta ne bayan Iwuanyanwu ya bukaci a bashi dama ya yi ganawar sirri da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a yayin da ya kai ziyarar ban girma a jihar.

Kema ta fusatta sosai bisa bukatar ganawar da Iwuanyanwu ya nema inda ya ce abin kunya ne da kuma tsantsagwaron son kai.

Abun kunya: An yi baran-baran tsakanin shugabannin PDP a wata jiha saboda ziyarar Atiku

Abun kunya: An yi baran-baran tsakanin shugabannin PDP a wata jiha saboda ziyarar Atiku

A cewarta, Atiku Abubakar ya kai ziyara jihar ta Imo ne saboda ya gana da dukkan shugabanin jam'iyyar kuma ba dai-dai bane wani ya nemi ya yayi babakere kamar saboda shi aka shirya ziyarar.

KU KARANTA: Bayan kai ruwa rana a baya, yanzu Kwankwaso zai ziyarci Kano

Jim kadan bayan gama musayar maganganu tsakanin Iwuayanwu da saura jiga-jigan jam'iyyar da suka hallarci taron, Kema, Ihedioha da Onyereri da masu goyon bayansu sun fice daga taron cikin fushi duk kuwa da irin kokarin rarashin su da Atiku ya yi.

Bayan taron, Atiku ya shaidawa manema labarai cewa aniyarsa na ganin ya kawo cigaba a Najeriya ce tasa har yanzu bai gajiya ba wajen fafutikarsa na zama shugaban kasar Najeriya.

Atiku wanda ya kai ziyarar tare da shugaban yakin neman zabensa kuma tsohon gwamnan jihar Ogun, Gbenga Daniel da sauran 'yan tawagansa ya ce ya san dabarun da zai bi wajen magance matsalolin da ke adabar Najeriya.

Ya ce ya kai ziyara ne jihar saboda ya gana da shugabanin jam'iyyar PDP saboda zaben fidda gwani na jam'iyyar da ke tafe nan gaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel