2019: Bukola Saraki zai yi takara da Buhari

2019: Bukola Saraki zai yi takara da Buhari

Shugaban majalisar dattijai, Abubakar Bukola Sarki, zai yi takara da shugaba Buhari a zaben shekarar 2019 kamar yadda jaridar Bloomberg ta rawaito.

A cewar jaridar ta Bloomberg, Saraki ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shi a gidansa dake Abuja: “Ina tuntuba kuma ina da karsashin yin takara. Na san cewar zan kawowa Najeriya canjin da take bukata,” a kalaman Saraki.

A ‘yan kwanakin da suka wuce ne Saraki ya fita daga jam’iyyar APC tare da komawa PDP, jam’iyyar da a cikinta ya zama gwamna a jiharsa ta Kwara sannan kuma ya zama Sanata.

2019: Bukola Saraki zai yi takara da Buhari

Bukola da Buhari

Ana alakanta fitar Saraki daga APC da niyyarsa ta son yin takarar shugaban kasa.

Saraki ya shiga jerin su Atiku, Kwankwaso, Makarfi, Lamido, Tanimu Turaki, Dankwambo da Tambuwal, da suke burin yiwa PDP takarar shugaban kasa.

DUBA WANNAN: Hukumar zabe (INEC) ta nemi biliyan N6bn domin ciyar da 'yan sanda lokacin zaben 2019

A ranar Litinin ne Saraki, ya ziyarci tsohon shugaban kasa Obasanjo inda suka shafe kusan sa’o’i biyu suna tattaunawa. Saraki ya ziyarci Obasanjo ne a gidansa dake hade da dakin karatun da ya gina a garin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Saraki ya isa gidan na Obasanjo ne da misalign karfe 5:30 na yamma cikin bakar babbar mota kirar Toyota Land Cruiser tare da wasu jami’an tsaron sa kuma ya bar gidan da misalign karfe 7:12 na dare.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel