Aiki har gida: Shugaba Buhari ya kammala shirin yi ma Atibu Abubakar sha tara ta arziki (Hoto)

Aiki har gida: Shugaba Buhari ya kammala shirin yi ma Atibu Abubakar sha tara ta arziki (Hoto)

Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kammala shirin gyaran hanyar da ta taso daga garin Mayo Belwa, ta ratsa garuruwan Jada, Ganye da Tounga, duk a jihar Adamawa, don inganta sufuri da al’amuran noma a wannan yanki, inji rahoton Rariya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ita dai wannan hanya itace babbar hanyar da ta shiga cikin garin Ganye, garin da aka haifi tsohon mataimakin shugaban kasa, dan takarar shugaban kasa kuma hamshakin Attajiri, Alhaji Atiku Abubakar.

KU KARANTA: Hajji ibadar Allah: Gwamnatin kasar Birtaniya ta tura Sojojinta don gabatar da aikin Hajji

Aiki har gida: Shugaba Buhari ya kammala shirin yi ma Atibu Abubakar sha tara ta arziki (Hoto)

Aikin titin Ganye

Ita dai wannan hanya ta kwashe sama da shekara 15 a cikin mawuyacin hali, hatta a zaman mulkin gwamnatinsu Atiku Abubakar da Cif Olusegun Obasanjo basu gyara wannan hanya ba, duk da tsananin lalacewarta.

Ministan ayyuka, gidaje da lantarki, Babatune Raji Fashola ya bayyana cewar za’a fara wannan aiki ne a ranar 25 ga watan Agusta, kuma an bada shi akan kudi naira biliyan Ashirin da biyu da miliyan dari bakwai (N22.7bn).

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel