Ko kotu ba zata iya ceton Saraki ba - Oshiomhole

Ko kotu ba zata iya ceton Saraki ba - Oshiomhole

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole yace ko kotu ba zata iya ceto shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ba.

Oshiomhole ya bayyana hakan a jiya, Talata, 14 ga watan Agusta a Abuja lokacin da kwamitin jam’iyyar ta gana da masu ruwa da tsaki a maalisar dokoki kasar.

An gudanar da taron ne a ranar da ya kamata ace an dawo zaman majalisar dokokin kasar domin duba kasafin kudin zaben 2019 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar.

Ko kotu ba zata iya ceton Saraki ba - Oshiomhole

Ko kotu ba zata iya ceton Saraki ba - Oshiomhole
Source: UGC

Oshiomhole yace za’a tsige Saraki daidai da doka, cewa ba zai yiwu ya jagoranci majalisa ba alhalin APC na da sanatoci 5 yayinda PDP ke da sanatoci 49.

KU KARANTA KUMA: Halin ba sani ba sabo: Ministoci sun cika da tsoron Osinbajo

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, Shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki ya nada Earl Osaro Onaiwu mai shekaru 59 a matsayin jami’in sadarwa na shugaban majalisar dattawa kan lamuran jiha.

Kakakin shugaban majalisar dattawan, Yusuph Olaniyonu a wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 15 ga watan Agusta, yace Onaiwu kwararren dan siyasa kuma jami’in gwamnati zai taimaka wajen kula da alaka tsakanin ofishin shugaban malisar dattawa da gwamnatocin jiha a fadin kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel