2019: Hukumar zabe (INEC) ta bukaci biliyan N6bn domin ciyar da 'yan lokacin zabe

2019: Hukumar zabe (INEC) ta bukaci biliyan N6bn domin ciyar da 'yan lokacin zabe

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC) ta bayyana cewar zata kashe Naira biliyan N6bn domin ciyar da jami'an 'yan sanda lokacin zaben shekarar 2019.

Hakan na kunshe ne cikin kasafin kudin hukumar da shugabanta, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya gabatar ga kwamitin majalisar wakilai a yau.

'Yan majalisar sun gayyaci hukumar ta INEC ne domin ta kare kasafin kudi biliyan N24bn da take bukatar majalisar ta sahale a ba ta bayan amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Har yanzu ana cigaba da ganawar tsakanin hukumar ta INEC da mambobin majalisa.

Zamu kawo maku karin bayani........

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel