Yanzu Yanzu: Bukola Saraki yayi sabon nadi a majalisar dattawa

Yanzu Yanzu: Bukola Saraki yayi sabon nadi a majalisar dattawa

Shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki ya nada Earl Osaro Onaiwu mai shekaru 59 a matsayin jami’in sadarwa na shugaban majalisar dattawa kan lamuran jiha.

Kakakin shugaban majalisar dattawan, Yusuph Olaniyonu a wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 15 ga watan Agusta, yace Onaiwu kwararren dan siyasa kuma jami’in gwamnati zai taimaka wajen kula da alaka tsakanin ofishin shugaban malisar dattawa da gwamnatocin jiha a fadin kasar.

Nadin na zuwa ne yayinda jam’iyyar All Progressives Congress ke ci gaba da matsa lamba kan Saraki yayi muramus daga matsayinsa.

Yanzu Yanzu: Bukola Saraki yayi sabon nadi a majalisar dattawa

Yanzu Yanzu: Bukola Saraki yayi sabon nadi a majalisar dattawa

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams, Oshiomhole ya bayyana cewa za’a tsige shugaban majalisar dattawa daidai da doka.

KU KARANTA KUMA: Halin ba sani ba sabo: Ministoci sun cika da tsoron Osinbajo

Oshiomhole yace jam’iyyar APC ta kammala shirin hanyar da zata bi domin tsige Saraki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel