El-Rufai ya kafa tarihi, ya mika ma majalisa naira biliyan 155.8 a matsayin kasafin kudin shekarar 2019

El-Rufai ya kafa tarihi, ya mika ma majalisa naira biliyan 155.8 a matsayin kasafin kudin shekarar 2019

Tun ran gini tun ran zane, inji masu iya magana, kuma dama ai ba’a fafe gora ranar tafiya, anan Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai ne ya mika kasafin kudi na shekarar 2019 ga majalisar dokokin jihar Kaduna.

Kamar yadda doka ta tanadar, ana bukatar gwamana ya mika ma majalisa kasafin kudin don su amince da shi, ta hanyar gayyato kwamishinonin maa’ikatu da shuwagabannin hukumomin da abin ya shafa domin su tsatstsage ma majalisar bayanai da hujjoji.

KU KARANTA: Zuba hannun jari: Yan kasuwar Turkiyya zasu kafa matatar man fetir a Najeriya

Da zarar majalisar ta kammala jin bahasi daga kwamishinoni da shuwagabannin hukumomin, idan har sun gamsu da bayanan da suka samu, sai su amince da kasafin ya zama doka, daga nan sai a mayar ma gwamna don ya rattafa hannu akan dokar, shike nan sai a fara aiwatar da ita.

A wannan karo El-Rufai ya mika kasafin kudi na naira biliyan dari da hamsin da biyar da miliyan dari takwas (N155,800,000,000) wanda yake hasashen gwamnatin za ta kashe tun daga albashin ma’aikata zuwa kudaden gudanar da ayyukan cigaba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an raba kasafin kudin gida biyu, bangaren albashi da bangaren manyan ayyuka, a wannan kasafin, Albashi ya samu naira biliyan N62.3, yayin da bangaren manyan ayyuka ya samu naira biliyan 93.5.

Al’amuran kiwon lafiya da harkar ilimini ne suka kwashi kaso mafi tsoka a kasafin kudin shekarar 2019, inda Ilimi ya samu kasha 27.5, yayin da kiwon lafiya ya samu kasha 15.02.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel