Dogara ya bayyana Matsalar dake kawo naƙasun Cigaban harkokin wasanni a Najeriya

Dogara ya bayyana Matsalar dake kawo naƙasun Cigaban harkokin wasanni a Najeriya

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, Kakakin Majalisar wakilai Mista Yakubu Dogara, ya bayyana naƙasun dake haifar da rashin ci gaba a harkokin wasanni cikin kasar nan ta Najeriya.

Shugaban na majalisar wakilai yake cewa, rashin kyakkyawan jagoranci, tsararan manufofi da kuma musamman halin ko oho daga bangaren gwamnati ke haifar da rashin ci gaba a harkokin wasanni da nishadantar wa a kasar nan.

Dogara ya bayyana hakan ne yayin taron kasa kasa da aka gudanar kan harkokin wasanni wanda kwamitin masu ruwa da tsaki na majalisar sa suka dauki nauyin shiryawa cikin babban birnin kasar nan a ranar Talatar da ta gabata.

Dogara ya bayyana Matsalar dake kawo naƙasun Cigaban harkokin wasanni a Najeriya

Dogara ya bayyana Matsalar dake kawo naƙasun Cigaban harkokin wasanni a Najeriya

Ya ci gaba da cewa, bai kamata rawar da gwamnati ke takawa ta taƙaita kadai wajen tanadar kudaden gudanar da wasanni ba inda yayi kira akan ta dauki nauyin shimfida tsare-tsaren da za su tabbatar da ci gaban gami da bunkasar wasanni.

KARANTA KUMA: Uba da 'Da sun yi taron dangin keta haddin wata Budurwa 'Yar shekara 13 a jihar Benuwe

Ya kara da cewa, Najeriya na da mashahuriyar hazaka ta fuskar wasanni wanda masu sharhi sun bayyana cewa rashin taka rawar gani daga bangaren gwamnati ke sanadiyar rashin ci gaban ta.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ko shakka ba bu yana da wadatacciyar cancantar kasancewa shugaban kasar Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel