Fadar shugaban kasa tayi Karin haske a kan batun Karin wa’adin hutun Buhari

Fadar shugaban kasa tayi Karin haske a kan batun Karin wa’adin hutun Buhari

Fadar shugaban kasa ta bayyana rahotannin dake yawo a kafafen yada labarai a kan cewar shugaba Buhari ya kara wa’adin hutun kwanaki 10 da yake yi a kasar Ingila a matsayin maras tushe balle makama.

Rahoton da ake yadawa a dandalin sada zumunta na nuni da cewar tuni shugaba Buhari ya aike da wasikar batun karin wa’adin hutun nasa ga majalisa.

Sai dai a wani sako da fadar shugaban kasa ta fitar a shafinta na Tuwita a daren jiya, Talata, tayi watsi da batun tare da bayyana cewar jama’a na yada tsohon labara ne da ya faru tun watan Fabarairu na shekarar 2017.

Fadar shugaban kasa tayi Karin haske a kan batun Karin wa’adin hutun Buhari

Buhari

A saboda haka ne fadar ta shugaban kasa ta nemi duk ‘yan kasa nagari da su yi watsi da rahoton tare da daina yada shi.

DUBA WANNAN: An karrama Aisha Buhari da digirin girmamawa a kasar Koriya (Hotuna)

A ranar 3 ga watan Agusta ne shugaba Buhari ya bar Najeriya domin yin hutu na kwana 10 a birnin Landan na kasar Ingila. Hutun na kwana 10 zai shafi ranakun aiki ne kawai kamar yadda mai taimakawa Buhari a bangaren yada labarai, Femi Adesina, ya sanar a ranar 1 ga watan Agusta.

A yayin da yake hutu, mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, zai jagoranci lamuran gudanar da harkokin gwamnati kamar yadda doka ta tanada,” a cewar Mista Adesina.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel