Fulani makiyaya sun dauki wani mataki da zai hana rigawa tsakaninsu da manoma

Fulani makiyaya sun dauki wani mataki da zai hana rigawa tsakaninsu da manoma

- Rikicin makiyaya da manoma ya sha lakume rayuka da dukiya mai tarin yawa a kasar nan

- 'Bari biyun sun kasance ma'abota daukar fansa a duk lokacin da suke zargin an yi musu laifi

- Amma sai dai da alama wannan daukar doka a hannu na daf da zuwa karshe matukar a kabi shawarar da wani babba a kabilar Fulanin ya bayar

Sarkin Chanchanga (Ardo) Malam Abdullahi Babayo yayi kira ga ‘yan uwansa makiyaya akan su daina tura yara kanana kiwo don kaucewa rigima da manoma.

Babayo wanda shi ne Sarkin Chanchanga da kuma masarautar Shaku dake garin Minna na jihar Niger, yayi wannan kira ne a yau laraba yayin da yake tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN).

Fulani makiyaya sun dauki wani mataki da zai hana rigawa tsakaninsu da manoma

Fulani makiyaya sun dauki wani mataki da zai hana rigawa tsakaninsu da manoma

Ya ce in har makiyayan zasu daina tura yara kanana kiwo tabbas za a samu raguwar fadace-fadace dake aukuwa.

KU KARANTA: Alhamdulillah: Farashin kayan abinci ya yi rugu rugu a wata jihar Arewacin Najeriya

"Gaskiya abin dubawa ne ace yaro karami ne zai fito kiwo da garken shanu masu tarin yawa".

"Rayuwarsa dama ta shanun da yake kiwo zasu iya zama cikin hadari, saboda masu kwacen shanu sukan far musu cikin ruwan sanyi".

"Sau da dama manoma abin yakan bata musu rai idan suka ga yaro karami yana kiwon shanu masu tarin yawa. Amma hankalinsu ya kan kwanta idan suka mai kiwo musamman babba yana kora shanun inda ciyawa take, ko ba komai sun san abinda suka suka ba abinda zai same shi" ya bayyana.

Fulani makiyaya sun dauki wani mataki da zai hana rigawa tsakaninsu da manoma

Fulani makiyaya sun dauki wani mataki da zai hana rigawa tsakaninsu da manoma

Sarkin Fulanin ya yi kira ga su manoman kansu cewa ya kamata su guji yin noma ko shuka akan hanyar da suka san cewa shanu na bi, domin samar da dorarren zaman lafiya.

"Manoma sun dogara ne akan yin noma, su kuma makiyaya sun dogara da kiwo ne, to dan haka ya kamata kowane ya girmama rayuwar wani dan a samu makobtaka mai kyau a tsakani".

"Ya kamata kowane bangare ya manta da wani abu da ya taba faruwa domin samar da zaman lafiya da kuma cigaban kasar nan" A cewar Ardo.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel