Ba bu ƙosawa amma na cancanci zama Shugaban 'Kasar Najeriya - Atiku

Ba bu ƙosawa amma na cancanci zama Shugaban 'Kasar Najeriya - Atiku

A ranar Talatar da ta gabata ne tsohon Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, yayi watsi kan yada gora da ake yi a kansa na cewar ya matsanta tare da ƙosawa sai ya zama shugaban kasar nan ta Najeriya a zaben 2019.

Tsohon Mataimakin shugaban kasar yake cewa, duk da ikirarin da masu adawa ke yi na cewar ya matsanta sai ya zama shugaban kasa, ko shakka ba bu ya cancanci tsayawa takara a zaben 2019 gami da kyawawan manufofi da akidu domin magance matsaloli gami da kalubalai da kasar nan ke fuskanta.

Ba bu ƙosawa amma na cancanci zama Shugaban 'Kasar Najeriya - Atiku

Ba bu ƙosawa amma na cancanci zama Shugaban 'Kasar Najeriya - Atiku

Manemin tikitin takarar jam'iyyar PDP ya bayyana hakan ne yayin da ziyarci jakadun jam'iyyar reshen jihar Edo domin neman goyon bayan su sakamakon gabatowar zaben fitar da gwani na jam'iyyar da za a gudanar a watan Satumba.

KARANTA KUMA: An rasa Jami'an Tsaro 30 cikin wata guda a Najeriya - Kwamishinan 'Yan sanda

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Turakin na Adamawa ya kuma bayyana damuwar sa dangane da yadda Najeriya ta tabarbare tare da koma baya cikin shekaru ukun da suka gabata.

A yayin da yake tuhumar gwamnatin jam'iyyar APC dangane da yadda al'ummar kasar ne ke cikin halin kakanikayi, Atiku ya bayyana cewa zaman lafiya yana tabbatuwa cikin kowace kasa matukar adalci da aikin yi za su wadatu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel