Ku tabbatar da cewa majalisa ta dawo – Oshiomole ga yan majalisan APC

Ku tabbatar da cewa majalisa ta dawo – Oshiomole ga yan majalisan APC

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC),ya yi kira gay an majalisan jam’iyyarsa suyi iyakan kokarinsu wajen tabbatar da cewa majalisa ta dawo zama.

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da kakakin majalisan dokokin, Yakubu Dogara, sun daatad da zaman majalisan tun lokacin da jami’an DSS suka hana shugaban majalisan da mataimakinsa, Ike Ekweremadu, fita daga goidajensu.

Shugaban jam’iyyar APC ya soki wannan mataki inda yace kulle majalisa na dawo da hannun agogo baya.

Ya yi wannan jawabi ne a Sheraton Hotel da ke Abuja ind aya gana da Sanatocin jam’iyyar da uma mambobin majalisar wakilai.

Ku tabbatar da cewa majalisa ta dawo – Oshiomole ga yan majalisan APC

Ku tabbatar da cewa majalisa ta dawo – Oshiomole ga yan majalisan APC

Yace: “Ina mika kokon barata ga sanatocin da mambobin majalisar wailar tarayya bisa ga alkawarin aiki ga kasan da kukayi, ku yi du kami yiwuwa wajen tabbatar da cewa majalisa ta dawo saboda a samu daman tattauna manyan abubuwan da suka shafi cigaban kasa.

Saboda a yanke shawara kan abubuwan kada gwamnatin Najeriya ta fuskanci matsala.”

KU KARANTA: Wani makiyin addinin musulunci ya kutsa kai da mota cikin masallacin juma'a

Shugaban jam’iyyar ya ce hanya daya tilo ne da ba za’a tsige Saraki ba kuma shine ya dawo jam’iyyar APC kuma hakan ba zai yiwu ba.

Ya kara da cewa zuwa kotun Bukola Saraki ba zai taimaka masa wajen hana tsigeshi saboda kotu a tada karfin zabawa yan majalisa shugaba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel