Yanzu-yanzu: Yan majalisa sun shiga ganawar gaggawa da hukumar INEC

Yanzu-yanzu: Yan majalisa sun shiga ganawar gaggawa da hukumar INEC

Kwamitin majalisar wakilan tarayya kan harkokin gudanar da aben sun shiga ganawa da jami’an hukumar gudanar da zabe ta asa mai zaman kanta wato INEC da safen nan a zauren majalisa.

Shugaban hukumar INEC, farfesa Mahmoud Yakubu, ne ya jagoranci sauran jami’an hukumar domin muqabala kan bukatan kudin da suk mika na gudanar da zaben 2019.

Kwamitin karkashin jagorancin Mrs Aisha Dukku zasu yi tambayoyi don tabbatar da gaskiyan abubuwan a hukumar INEC ta bukaci yi da kudi sama da Biliyan N240bn.

Yanzu-yanzu: Yan majalisa sun shiga ganawar gaggawa da hukumar INEC

Yanzu-yanzu: Yan majalisa sun shiga ganawar gaggawa da hukumar INEC

Har yanzu dai ba’a san lokacin da majalisar dokokin tarayyar za ta dao bakin aiki ba domin rikicin da ke fauwa tsakanin jam’iyyun APC da PDP.

Shugabancin jam’iyyar APC ta lashi takobin cewa idan har majalisa ta dawo hutu, sai an tsige shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki tun da ya bar jam’iyya mai rinjaye a majalisan.

KU KARANTA: Gaskiyar lamari PDP bata da niyar chanja suna - Lamido

Zuwa yanzu, jam'iyyar APC na da kimanin sanatoci 57 kuma jam'iyyar PDP na da kasa da hakan. Lauyoyi sun bayyana cewa sai sanatoci 73 ne zasu iya tsige shugaban majalisar bisa ga doka.

Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa suna tattaunawa da wasu sanatocin jam'iyyar PDP wajen shawo kansu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel