Zaben fitar da gwani: Jam'iyyar APC ta fitar da tsarin yadda zata tunkari babban zaben 2019

Zaben fitar da gwani: Jam'iyyar APC ta fitar da tsarin yadda zata tunkari babban zaben 2019

A yayin cigaba da kokarin tunkarar zabukan gama-gari da za'a gudanar a shekarar 2019, jam'iyya mai mulki a Najeriya ta All Progressives Congress, APC ta fitar da tsarin jadawalin yadda zata gudanar da zabukan ta na fitar da gwani domin tunkarar zaben.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar jiya a garin Abuja dauke da sa hannun jami'in yada labaran ta mai rikon kwarya.

Zaben fitar da gwani: Jam'iyyar APC ta fitar da tsarin yadda zata tunkari babban zaben 2019

Zaben fitar da gwani: Jam'iyyar APC ta fitar da tsarin yadda zata tunkari babban zaben 2019

KU KARANTA: Kasashen duniya ba su son Buhari yayi tazarce

Legit.ng ta samu cewa jam'iyyar ta saka ranar 15 ga watan Satumba a matsayin ranar da za'a gudanar da zabukan fitar da gwani na 'yan majalisun jahohi a dukkan fadin kasar.

Sai kuma 19 ga watan Satuma a gudanar da na 'yan majalisun wakilai yayin da kuma 23 da kuma 28 ga wata za'a gudanar da na Sanatoci da gwamnoni sai kuma 6 ga watan Oktoba a gudanar da na shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel